logo

HAUSA

Sin da Saudiyya abokai ne na gaskiya bisa manyan tsare-tsare

2022-12-10 17:05:54 CMG Hausa

Shugabannin kasashen Sin da Saudiyya, sun daddale yerjejeniyar raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen 2, inda suka amince da daga matsayin shugaban kwamitin hadin gwiwa na manyan jami’an kasashen Sin da Saudiyya zuwa matsayin firaminista, kana Sin ta amince da maida kasar Saudiyya a matsayin wurin yawon shakatawa da Sinawa za su rika zuwa cikin tawaga, kuma kasar Saudiyya ta yi maraba da karin kamfanonin Sin da su shiga aikin raya masana’antun kasar.

A ranar 8 ga wannan wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Sarki Salman bin Abdul Aziz Al Saud na masarautar Saudiyya, kana ya yi shawarwari tare da firaministan kasar kuma yarima Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud. Inda bangarorin biyu suka cimma daidaito kan yadda za a sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu. Babban editan jaridar Al Riyadh ta kasar Saudiyya Hani Wafa ya wallafa wani sharhi dake cewa, wannan ziyara za ta sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin Saudiyya da Sin a dukkan fannoni zuwa wani sabon mataki, hakan zai taimaka wajen samar da kyakkyawar makoma kan dangantakarsu.

A jawabinsa, Sarki Salman na Saidiyya ya bayyana cewa, moriyar Sin ita ce moriyar Saudiyya. Wannan magana ta jawo hankalin kafofin watsa labaru da dama. Yayin ziyarar shugaba Xi, bangarorin biyu sun nuna goyon baya ga juna kan harkokin siyasa. Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana goyon bayan kasar Saudiyya da ta ci gaba da bin hanyar bunkasa kasa bisa yanayin kasar. Firaminista kuma yarima Muhammad shi ma ya nuna goyon baya ga kasar Sin sosai. A yanayin tinkarar sauye-sauye da kasa da kasa da yankuna ke fuskanta, Sin da Saudiyya sun nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, hakan zai tabbatar da raya dangantakar dake tsakaninsu a sabon zamani.

Zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Saudiyya zai kawo kyakkyawar fata ga jama’arsu, kana zai samar da karin gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da kuma samun bunkasuwa da wadata a duniya baki daya. (Zainab)