logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi shawarwari tare da manyan shugabannin kasar Saudiyya

2022-12-09 10:14:37 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sarkin masarautar Saudiyya, Salman bin Abdul Aziz Al Saud a fadarsa dake birnin Riyadh.

Xi ya ce, kasarsa ta mayar da Saudiyya a matsayin wata muhimmiyar kasa dake taka rawar gani a harkokin duniya, inda take fatan kara mu’amalar manyan tsare-tsare tare da Saudiyya, da zurfafa hadin-gwiwa a bangarori daban-daban, a wani kokari na kiyaye moriyarsu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

A nasa bangaren, sarki Salman ya yi marhabin lale da zuwan shugaba Xi, inda a cewarsa, yana matukar maida hankali kan raya dangantaka tare da kasar Sin, da kuma bayyana fatansa na samar da ci gaban huldodin kasashen biyu, bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni.

Shugabannin biyu sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar kulla dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni, tsakanin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da kasar Saudiyya, inda suka amince cewa, za su gana a kasashensu a kowace shekara.

A dai wannan rana, shugaba Xi ya yi shawarwari tare da yariman masarautar Saudiyya, kana firaministan kasar Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud, inda suka yarda cewa, za su daga matsayin shugabancin kwamitin hadin-gwiwar manyan jami’an kasashen biyu, zuwa matsayin firaminista.

Shugabannin biyu sun kuma halarci bikin mika wa juna takardun yarjeniyoyin hadin-gwiwar kasashensu, a fannonin da suka shafi raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da aikin shari’a, da ilimi, da makamashin hydrogen, da zuba jari, da gidajen kwana da sauransu.

Bayan shawarwarin, shugaba Xi ya halarci bikin maraba da yariman Muhammad ya shirya masa, a madadin sarkin Salman bin Abdul Aziz Al Saud. (Murtala Zhang)