logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Tunisiya da firaministan kasar Iraki

2022-12-09 17:41:14 CMG Hausa

Da safiyar yau Jumma’a 9 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Tunisiya Kais Saied, a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.

A yayin ganawar, Xi ya jaddada cewa, kasarsa na goyon-bayan Tunisiya, wajen bin tafarkin samar da ci gaba bisa hakikanin halin da kasar take ciki, da nuna adawa da shisshigin da sauran kasashe suka yi cikin harkokin gidan Tunisiya. Sin na kuma fatan yin kokari tare da Tunisiya, domin taimakawa ci gaban hadin-gwiwa da kasashen Larabawa, da ma Sin din da sauran kasashen Afirka baki daya.

A nasa bangaren kuwa, shugaban Saied na Tunisiya, ya taya Sin murnar cimma nasarar gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, inda ya ce, kasarsa na fatan yin kokari tare da Sin, don daga matsayin huldodin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. Kana, taron kolin kasashen Larabawa da kasar Sin karo na farko na da ma’anar tarihi, kuma Tunisiya za ta nuna kwazo wajen samar da ci gaba ga dangantakar kasashen Larabawa da kasar Sin.

A dai yau din, Xi Jinping ya kuma gana da firaministan kasar Iraki Mohammed Shia al-Sudani. (Murtala Zhang)