logo

HAUSA

Kawancen ’yan majalissar EAPA ya yi kira da a kara adadin kasafin noma domin yaki da yunwa

2022-12-09 12:52:14 CMG Hausa

Kawancen ’yan majalissar gabashin Afirka masu rajin samar da isasshen abinci mai gina jiki ko EAPA, ya yi kira ga gwamnatocin yankin, da su kara yawan kasafin kudi ga fannin noma da kiwo, domin shawo kan matsalar yunwa a yankin.

Kawancen na EAPA ya yi wannan kira ne yayin bude taron yini 3 a jiya Alhamis, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda.

Kawancen EAPA ya kunshi ’yan majalisun dokoki daga kasashen gabashin Afirka 9, wadanda a taron nasu na wannan karo, za su mayar da hankali wajen tattauna batutuwan da suka shafi rawar da ’yan majalissa za su iya takawa a fannin zuba jari a bangaren noman da iyalai ke gudanarwa, da dabarun jure wahalhalun samar da abinci da abinci mai gina jiki a yankin na gabashin Afirka.

Da yake tsokaci yayin bikin bude taron, shugaban kawancen na EAPA Abdi Ali Hassan, ya ce ’yan majalissa na da muhimmiyar rawar takawa a fannin samar da sauye-sauye da suka wajaba, na tabbatar da wadatuwar cimaka a nahiyar Afirka.

Abdi Ali Hassan, ya kuma yi kira ga daukacin ’yan majalissun da su yi amfani da karfin ikonsu, wajen karfafa gwiwar al’ummun da suke wakilta, ta yadda za su iya cin galabar kamfar abinci, da shawo kan matsalar karancin abinci mai gina jiki, ta hanyar samar da karin kudade ga ma’aikatu, da sauran sassa dake ba da hidima ga raya harkar noma.

A watan da ya gabata ne shirin abinci da aikin gona na MDD ko WFP, ya fitar da wata sanarwa dake cewa, fari dake addabar kasashen Kenya, da Habasha, da Samoliya, ya jefa al’ummun da yawansu ya kai mutum miliyan 22 cikin yanayi na karancin abinci. (Saminu Alhassan)