logo

HAUSA

An wallafa bayanin Xi Jinping a jaridar Saudiyya

2022-12-08 10:40:57 CMG Hausa

Bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, don halartar taron koli na farko, na Sin da kasashen Larabawa, da taron koli na Sin da kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko GCC, tare da kai ziyartar aiki a kasar, an wallafa bayanin da Xi ya rubuta a jairdar Riyadh, mai taken “Yaukaka dankon zumunta, samar da makoma mai haske”.

Bayanin ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, alakar Sin da Saudiyya na bunkasa yadda ya kamata. Kasar Sin za ta yi amfani da wannan dama, don karfafa dangantakar abuta tare da Saudiyya bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da kara hadin-gwiwa don nuna adawa da shisshigin da sauran kasashe ke yi, da neman ci gaba cikin ‘yanci. Kana, kasashen biyu za su yi kokari tare, don hade shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da “muradun samar da ci gaba na Saudiyya zuwa shekara ta 2030”. Bugu da kari, kasashen biyu, za su fadada mu’amala da juna a fannonin da suka shafi harkokin Majalisar Dinkin Duniya, da kasashen G20 da kungiyar hadin-kan Shanghai wato SCO da sauransu, a wani mataki na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, da samar da ci gaba a duk fadin duniya baki daya.

Bayanin Xi ya kuma ce, Sin babbar kasa ce dake kokarin shimfida zaman lafiya da ci gaba a duniya, da kara samar da sabbin damammaki ga kasa da kasa, ciki har da na Larabawa, don yaukaka dankon zumunta, da samar da makoma mai haske tare da ‘yan uwa kasashen Larabawa. (Murtala Zhang)