logo

HAUSA

Xi ya ba da amsa ga wakilan masu sha’awar koyon Sinanci na Saudiyya

2022-12-08 10:39:25 CMG Hausa

Kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da amsar sako ga wakilan masu sha’awar koyon Sinanci na kasar Saudiyya, inda ya kara karfafa zukatan matasan Saudiyya, domin su yi kokarin koyon Sinanci, ta yadda za su taimaka wajen zurfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Saudiyya, da ma tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.

A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, koyon harsuna na sauran kasashe, zai ingiza zumuncin dake tsakanin al’ummomin kasashen, da taka rawa kan gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya.

A kwanakin da suka gabata ne, matasan Saudiyya masu sha’awar koyon Sinanci sama da 100, suka aike da wasiku ga shugaba Xi domin shaida masa sakamakon da suka samu yayin da suke koyon Sinanci, inda suka bayyana cewa, suna son kara fahimtar kasar Sin, tare kuma da zurfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Saudiyya.

A halin da ake ciki yanzu, an riga an shigar da darasin Sinanci cikin manhajan ba da ilmi na Saudiyya, haka kuma an kafa sana’ar ilmi dake da nasaba da Sinanci a jami’ai 9 a kasar. (Jamila)