logo

HAUSA

Xi ya isa Riyadh domin halartar taron kolin Sin da kasashen Larabawa karo na farko

2022-12-08 10:33:15 CMG Hausa

A yammacin jiya Laraba, agogon kasar Saudiyya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Riyadh, fadar mulkin kasar, bisa gayyatar da sarki  Salman bin Abdul Aziz Al Saud na Saudiyya ya yi masa, domin halartar taron kolin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko, da taron kolin kasar Sin da hukumar hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf, da kuma kai ziyarar aiki a kasar ta Saudiyya. Manyan jami’an gwamnatin Saudiyya ne suka yiwa Xi maraba, yayin da sauka a filin jirgin saman Riyadh King Khaled cikin jirgin sama na musamman,

Daga baya shugaba Xi ya gabatar da wani jawabi a rubuce, inda ya nuna gaisuwa da fatan alheri ga gwamnati da al’ummar Saudiyya a madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, ya kuma yi nuni da cewa, tun bayan da kasashen Biyu wato Sin da Saudiyya suka daddale huldar diplomasiyya  shekaru 32 da suka gabata, huldar dake tsakaninsu ta samu ci gaba yadda ya kamata, har ta kai ga ingiza zaman lafiya da wadata a yankin. Yayin da yake ziyarar aiki a Saudiyya, Xi zai yi musayar ra’ayoyi da sarki Salman da yarima Mohammed, kan huldar sassan biyu da batutuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya da suke jawo hankulansu, domin ciyar da huldar kasashen biyu gaba. Kana Xi bayyana cewa, yana son yin kokari tare da kasashen Larabawa domin ciyar da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa zuwa wani sabon mataki. (Jamila)