logo

HAUSA

Labarai masu dumi-dumi a gasar cin kofin duniya ta Qatar

2022-12-08 20:27:37 CMG Hausa

Da yammacin ranar 3 ake gudana a kasar Qatar. Argentina da Netherlands sun nuna kwarewarsu ta zama manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya, inda suka doke Australia da Amurka bi da bi, kana za su hadu a zagayen kasashe 8 da suka yi nasarar zuwa zagaye wasan kwaf daya na gasar.

‘Yan wasan Netherlands Memphis Depay, Daley Blind da Denzel Dumfries ne, suka zura kwallaye a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, inda suka doke Amurka da ci 3-1 a wasan na yammacin ranar Asabar.

Lionel Messi da Julian Alvarez ne suka jefawa Argentina kwallayen da suka ba su nasarar kaiwa wasan daf da na kusa da na karshe, bayan da Argentina ta doke Australia da ci 2-1.

Da wannan sakamako, Argentina za ta fafata da Netherlands a filin wasa na Lusail a ranar Juma'a, domin samun gurbin zuwa wasan kusa da na karshe.

Litinin 5 ga wata ne, aka buga wasan daf da na kusa da na karshe, a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya FIFA da ake yi a Qatar, inda kungiyoyin kasashen Asiya 2, wato na Japan da na Koriya ta Kudu suka kara da Croatia da Brazil.

Yayin wasan Croatia da Japan an kai bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Croatia ta yi nasara da ci 4:2. Yayin da tawagar Koriya ta Kudu ta sha kashi da ci 4 da 1 a hannun Brazil.

Kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen Faransa da Ingila, da suka jima suna hamayya da juna, a bana ma sun sake haduwa a gasar cin kofin duniya dake gudana yanzu haka a Qatar, bayan da Faransa ta doke Poland, ita kuma Ingila ta samu nasara kan Senegal, a zagayen kungiyoyi 16 na gasar, wanda aka buga ranar Lahadi a filin wasa na Al-Thumama.

Kylian Mbappe ne ya ciwa Faransa kwallaye 2, cikin kwallaye 3 da Faransa ta zura a ragar Poland, inda aka tashi wasan ci 3 da 1.

Kafin hakan, Olivier Giroud ya zarce Thierry Henry da yawan kwallaye ga kasar Faransa, bayan da ya jefa ta sa kwallo, kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Da yake tsokaci kan nasarar da Faransa ta samu, Mbappe ya shaidawa manema labarai cewa "Muna farin cikin samu damar zuwa wasan kusa da na karshe. Wasa ne mai wahalar gaske. Mun taka leda ga abokan karawa masu karfi, amma duk da haka mun yi nasarar jefa kwallaye a lokaci mafi muhimmanci na wasan. Duk da cewa ba mu taka wasa yadda ya kamata ba, mun yi nasara, kuma muna farin ciki da hakan”.

Ya zuwa yanzu, Mbappe mai shekaru 23 a duniya, ya riga ya ci kwallaye 5 a gasar ta cin kofin duniya, wanda hakan ya ba shi jimillar kwallaye 9 a gasar cin kofin duniya da ya halarta.

Mbappe ya kara da cewa, "Bana tunanin wata kyautar bajimta, kamar kwallon zinari, ko takalmin zinari da ake baiwa taurarin ‘yan wasa. Muhimmin abu shi ne mu yi nasarar lashe kofin duniya. A yanzu, wasan kusa da na karshe shi ne muhimmin abun dake gaban mu. Shi ne abun da nake mafarkin lashewa. Na zo ne na yi nasarar lashe kofi, na kuma taimakawa kasa ta, ba wani abu daban ba".

A daya wasan kuwa, Ingila ta yi nasarar zura kwallaye 3 a ragar Senegal, inda kyaftin din Ingila Harry Kane, wanda kuma shi ne mai rike da takalmin zinari na gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Rasha a shekarar 2018, ya fara jefa kwallo a ragar Senegal, kafin daga bisani Jordan Henderson, da Bukayo Saka su kara kwallaye daidaiya.

Game da yadda yake ganin za ta wakana a wasan su na gaba da Faransa, a ranar Asabar a filin wasa na Al Bayt, kocin kungiyar Ingila Gareth Southgate, ya ce “Faransa na da ‘yan wasa kwararru, wadanda suka kafa tarihi mai karfi a wannan gasa, don haka ko shakka ba bu, sai mun zage-damtse kafin mu kai ga nasara".

A ranar Talata ne, aka ci gaba da wasan neman shiga zagayen kasashe 8 da za su fafata a gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar. Kasar Morocco ta doke Spaniya wadda ake sa ran za ta lashe kofin gasar, inda aka kammala wasan ta zama ci 3 da 0 bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida. A daya wasan kuma kasar Portugal ta doke Switzerland da ci 6:1, inda ‘dan wasan Portugal Goncalo Ramos ya jefa kwallaye uku rus.

 Yanzu Portugal da Morocco za su fafata a wasan kusa da na karshe.