logo

HAUSA

MDD: Sama da yaran Somaliya miliyan 2.6 ne aka yiwa rigakafin cutar shan inna da kyanda

2022-12-08 11:03:47 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) tare da hadin gwiwar asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) sun bayyana cewa, an yiwa yara miliyan 2.61 allurar rigakafin cutar kyanda da shan inna a kasar Somaliya.

Hukumomin MDDr sun bayyana cewa, shirin hadaka na rigakafi a fadin kasar, wanda aka kaddamar a watan Nuwamba a gabar da kasar ke fama da mummunan fari, na fatan kaiwa ga yara ’yan kasa da shekaru biyar, domin kubutar da su daga cututtukan da za a iya rigakafi, kamar su kyanda da polio ko shan Inna.

Wakilin WHO a Somaliya Mamunur Rahman Malik, ya ce hukumar kula da lafiya ta MDD, tana amfani da dukkan albarkatun da take da su, da kuma sabbin hanyoyin da suka dace, kamar gamgamin gama-gari, amfani da makamashin hasken rana a cibiyoyin kiwon lafiya don kula da tsarin sanyaya alluran riga-kafi, da hada kan al'ummomin yankin, don ceton rayukan miliyoyin yaran Somaliya, da suka cancanci samun rayuwa mai haske da koshin lafiya.

A cewar MDD, rikicin jin kai da ya haifar da tashe-tashen hankula, da tsawon lokaci na fari, da yawaitar al’umma na kauracewa matsugunansu a Somaliya, ya jefa yara fiye da miliyan 3.6 'yan kasa da shekaru biyar cikin hadari, yayin da garkuwar jikinsu ke hadarin yin kasa, kuma lalurar na karuwa kusan a kowane wayewar gari. (Ibrahim Yaya)