logo

HAUSA

Li Keqiang Ya Gana Da Shugaban Bankin Duniya

2022-12-08 21:50:59 CMG HAUSA

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban bankin duniya David Malpass a yau Alhamis, yayin taro na 7 na rukunin "1+6" dake gudana a birnin Huangshan na lardin Anhui.

Yayin ganawar tasu, firaminista Li ya ce, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasa, yayin da ake aiwatar da matakai mafiya dacewa na kandagarki da yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce Sin za ta aiwatar da tsare-tsare masu inganci, na kandagarki da shawo kan annobar, tare da na bunkasa tattalin arzikin ta, kana za ta kare rayukan al’umma, tare da wanzar da ayyukan samar da hajoji, da kyakkyawar rayuwa ta yau da kullum.

A nasa bangare, Mr. Malpass ya ce, bankin duniya na yabawa matakin kasar Sin, na daidaita matakan kandagarki da yaki da annobar, bankin yana kuma maraba da matakan Sin na kara bude kofa ga waje, yana kuma dora muhimmanci sosai ga abokan huldar sa na samar da ci gaba, kuma bankin a shirye yake, ya zurfafa hadin gwiwa a fannonin cinikayya, da yada ilimi, domin ingiza ci gaban bai daya na duniya.

A dai wannan rana, Li ya kuma gana da babbar daraktar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva, da babban sakataren kungiyar bunkasa ci gaban tattalin arziki da samar da ci gaba ko OECD Mathias Cormann.  (Saminu Alhassan)