logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon murnar cika shekaru 30 da kafa kungiyar masana tarihin kasar Sin

2022-12-08 14:03:13 CMG Hausa

Yau Alhamis, babban sakataren kwamitin kolin JKS, shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin kolin soja na kasar Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar cika shekaru 30 da kafa kungiyar masana nazarin tarihin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, inda ya isar da gaisuwa da fatan alheri ga masanan kungiyar da daukacin ma’aikatan nazarin tarihin kasa dake fadin kasar.

An kafa kungiyar ce da nufin ingiza aikin nazari da yada manufa da kuma koyar da ilmin tarihin kasar ta Sin. (Jamila)