logo

HAUSA

Ta yaya ake kare matasa da kananan yara daga kasa ganin abubuwa masu nisa?(A)

2022-12-07 18:49:19 CMG HAUSA

 

A shekarun baya, yawan matasa da kananan yara masu fama da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa na ta karuwa a duk fadin duniya. Tun bayan barkwar annobar cutar COVID-19, lokacin motsa jiki a wajen daki da kuma lokacin koyon ilmi ta hanyar amfani da kayan laturoni na zamani sun karu, don haka yawan matasa da kananan yara masu fama da matsalar ya ci gaba da karuwa. To, ta yaya za a taimaka wa matasa da kananan yara su kare idanu da girma yadda ake fata? Masana ilmin cututtukan idanu a kasa da kasa sun ba da nasu shawarwari kan yin amfani da idanu ta hanyar kimiyya.

Da farko, wajibi ne a kula da yanayin zama yayin da ake karatu ko rubutu. Hadaddiyar kungiyar likitoci masu kula da cututtukan idanu ta kasar Japan ta ba da shawarar cewa, ana bukatar kula da yanayin zama yayin da ake karatu ko rubutu don rigakafin kasa ganin abubuwa masu nisa. A zauna tsaye, da tabbatar da tazarar da ke tsakanin idanu da littafi ya kai misalin centimita 30. Masana daga kasar Koriya ta Kudu kuma sun ba da shawarar cewa, yayin da ake ba da ilmi ta yanar gizo, kamata ya yi dalibai su kara sanin yadda suke amfani da kayan laturoni na zamani ta hanyar da ta dace, alal misali, tabbatar da nisan da ke tsakanin idanu da kayan ya kai centimita a kalla 50.

Ban da haka kuma, wajibi ne a kaurace wa barin idanu su gaji. Masana daga kasar Japan sun nuna cewa, ya fi kyau a huta minti 5 zuwa 10 a ko wace awa 1 da matasa da kananan yara suke karatu ko rubutu, kana a kaurace wa daukar minti fiye da 40 ana wasa kan kayan laturoni na zamani.

Masana na kasar Rasha sun bada shawarar cewa, bai kamata kananan yara ‘yan kasa da shekaru 4 su yi amfani da kayan laturoni na zamani ba. ‘Yan kasa da shekaru 8 kuma bai kamata a bar su yi amfani da kayan fiye da minti 15 zuwa 20 ba a ko wace rana. Sa’an nan kuma, bai kamata ‘yan sama da shekaru 12 su yi amfani da kayan fiye da awoyi 2 ba a ko wace rana.

Masu karatu, ko kun san wata ka'ida mai saukin aiwatarwa dangane da kiyaye idanu? Wato 20 da 20 da 20. Madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani kan ka’idar, inda ta ce, yayin da ake amfani da kayan laturoni na zamani, ya fi kyau a dan huta dakikoki 20 a kau da ido daga kayan cikin ko wadanne minti 20, a kalli abubuwan da ke da nisan kafa 20, kwatankwacin mita 6. (Tasallah Yuan)