logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya isa Riyadh

2022-12-07 21:44:27 CMG HAUSA

Da yammacin ranar 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, inda zai halarci taron koli na farko, na Sin da kasashen Larabawa, da taron koli na Sin da kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko (GCC), wanda zai gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. Kaza lika shugaban na Sin zai gudanar da ziyarar aiki a masarautar ta Saudiyya. (Tasallah Yuan)