logo

HAUSA

Firaministan Sin Zai Gana Da Jagororin Manyan Hukumomin Hada-hadar Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa

2022-12-07 20:48:24 CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai yi zama na 7, tare da jagororin hukumomin hada-hadar tattalin arziki na kasa da kasa mai lakabin "1+6", a birnin Huangshan na lardin Anhui.

Yayin taron na gobe Alhamis da jibi Jumma’a, firaministan Li Keqiang, zai gana da shugaban bankin duniya David Malpass, da babbar manajar asusun ba da lamuni na IMF Kristalina Georgieva, da babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya Ngozi Okonjo-Iweala.

Kaza lika zai tattauna da babban daraktan kungiyar kwadago ta duniya Gilbert F. Houngbo, da babban sakataren hukumar bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da samar da ci gaba Mathias Cormann, da jagoran hukumar daidaita harkokin hada-hadar kudade Klaas Knot.

Kakakin ta kara da cewa, taken tattaunawar ta wannan karo shi ne  "Karfafa hadin gwiwar sassa daban daban, a fannin samar da ci gaban duniya na bai daya", kuma jami’an da za su halarci zantawar, za su mai da hankali ga musayar ra’ayoyi, da shawarwari, game da batutuwan da suka hada da gina budadden tsarin tattalin arzikin duniya, da dabarun bunkasa farfadowa da bunkasar tattalin arzikin duniya, da kuma kwazon kasar Sin a fannin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, ta hanyar zurfafa gyare-gyare.   (Saminu Alhassan)