logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin zai halarci taron kolin kasashen Sin da Larabawa, da Sin da GCC, da kai ziyara kasar Saudiyya

2022-12-07 10:53:34 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chungying, ta sanar a yau cewa, daga yau Laraba 7 zuwa 10 ga watan Disamba, bisa gayyatar Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci taron koli na farko na kasar Sin da kasashen Larabawa, da taron koli na Sin da kasashen kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC) da za a shirya a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, kana zai kai ziyarar aiki kasar Saudiyya.  (Ibrahim)