logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga da dama a arewacin kasar

2022-12-07 12:17:15 CMG Hausa

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa, sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama a wani samame da suka kai a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Kwamishinan ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata cewa, an tabbatar da kashe ‘yan bindiga da dama, kana wasu da dama kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu, a lokacin da sojojin suka kai farmaki a dazukan yankin Giwa dake jihar a ranar Litinin.

Aruwan, ya bukaci hadin kan mazauna jihar game da wadanda ake zargi da neman kulawar likitoci, saboda raunin harbin bindiga, watakila suna iya zama ’yan bindigan da suka tsare ne.(Ibrahim)