Yadda kasar Sin ke kara inganta matakan kare hakkin dan-Adam
2022-12-07 09:20:37 CMG Hausa
A kwanakin baya ne, asusun raya aikin kare hakkin dan Adam na kasar Sin, da kungiyar manyan masanan kasar ta kamfanin dillancin labarai na Xinhua, suka fitar da rahoton masana mai taken “Tabbatar da dadin rayuwar al’ummar kasa: Kokarin da ake yi wajen cimma ra’ayin kare hakkin dan Adam a kasar Sin a zamanin yanzu” cikin harsunan Sinanci da Turanci.
Rahoton ya yi bayani kan muhimmancin kokarin kare hakkin dan Adam da kasar Sin take yi, wajen ingiza aikin kyautata yanayin hakkin dan Adam da kasashen duniya ke ciki, da kuma ciyar da aikin kare hakkin dan Adam gaba daga dukkanin fannoni.
Ana iya bayyana ra’ayin kare hakkin dan Adam na kasar Sin kamar haka: “Hakkin dan Adam shi ne tabbatar da jin dadin rayuwar al’ummar kasa”. Rahoton ya bayyana cewa, ya dace a nace kan manufar kiyaye moriyar al’ummar kasa, kuma sabbin matakan kare hakkin bil Adam da kasar Sin ta dauka, sun kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa.
Kana rahoton ya kara da cewa, ya dace a kara karfafa cudanya tsakanin mabambanta wayewar kai, ta yadda za a kyautata yanayin kare hakkin dan Adam da kasashen duniya ke ciki, da kuma kafa tsarin tafiyar da harkokin hakkin bil Adam na kasa da kasa mai adalci, da gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya.
Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ta yi nasarar inganta rayuwar al’ummar Sinawa ta hanyar tsame su daga matsalar kangin talauci, da samun matsakaiciyar wadata a dukkan fannoni. Wannan a cewar masu fashin baki, shi ne kare hakkin bil-Adam. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)