logo

HAUSA

Kamfanin Huawei na kasar Sin ya samar da ilimin ICT ga daliban kwalejin Habasha

2022-12-07 10:20:28 CMG Hausa

Katafaren kamfanin fasahar sadarwa na kasar Sin Huawei, karkashin shirinsa na yara manyan gobe ko Future Program a Turance, ya ba da horo da musayar kwarewa kan fasahar sadarwa (ICT) ga daliban jami'o'in kasar Habasha.

Kamfanin Huawei ya bayyana a cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar jiya Talata cewa, shirin, wanda na tsawon mako guda, ya samar da horo ga dalibai 66 daga jami'o'in Habasha 12. Bugu da kari, an gudanar da bikin yaye dalibai ta yanar gizo a gaban jami'an ma'aikatar ilimi ta Habasha.

A cewar sanarwar, daliban sun koyi fasahar zamani da sabbin abubuwa daga fitattun malamai a wasu muhimman fannoni kamar 5G, da sadarwar yanar gizo, da adana bayanai.

A shekarar 2008 ne, kamfanin Huawei ya kaddamar da shirin yara manyan gobe, don tallafawa wajen zakulo masu hazaka a cikin gida a fannin fasahar zamani a cikin al'ummomi a duniya baki daya. Tun daga shekarar 2016, ana gudanar da shirin kowace shekara a Habasha, inda dalibai sama da 200 ke halarta. (Ibrahim Yaya)