logo

HAUSA

Jami'an kahon Afirka sun jaddada aniyar tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin

2022-12-07 10:34:53 CMG Hausa


Manyan jami’ai daga kasashen yankin kahon Afirka, sun kuduri aniyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaban bai daya, bayan shafe shekaru da dama ana fama da rikici da bala'o'i na muhalli.

A jawaban da suka gabatar ta kafar bidiyo yayin wani taron tattaunawa da cibiyar Brookings ta shirya, jami'an sun ce magance matsalolin tsaro da muhalli, shi ne jigon kokarin bunkasa tattalin arziki da hadin kai a yankin.

Ministan shari'a na Habasha Gedion Timothewos ya bayyana cewa, yankin kahon Afirka na fama da kalubale iri-iri, da suka hada da rikice-rikicen cikin gida, da fari, da tilastawa jama’a gudun hijira, da ta'addanci, kuma samar da mafita na dogon lokaci, ya rataya ne a kan bijiro da kudiri na siyasa, da hadin gwiwar yanki, da 'yan kasa.

Uwargida Monica Juma, mai baiwa shugaban kasar Kenya William Ruto shawara kan harkokin tsaro, ta ce gwamnatin kasar Kenya ta yi maraba da shirye-shiryen yankin da nufin magance tashe-tashen hankula, da tayar da zaune tsaye, da bala'o'i, da kuma rashin ci gaba da ake fuskanta a yankin. (Ibrahim Yaya)