logo

HAUSA

An gudanar da taron tunawa da marigayi Jiang Zemin

2022-12-06 15:45:05 CMG Hausa

Da safiyar yau Talata ne aka gudanar da taron tunawa da marigayi Jiang Zemin, wanda ya rasu yana da shekaru 96 a ranar 30 watan Nuwamban da ya gabata. 

An dai gudanar da taron ne a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin taron.

Tun a farkon taron, daukacin mahalarta sun yi shiru na mintuna 3, domin nuna alhanin rasuwar marigayi Jiang.  (Saminu Alhassan)