logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Bukaci Japan Da Ta Yi Taka Tsan-tsan Kan Kalamai Da Ayyukanta A Fannonin Soji Da Tsaro

2022-12-06 20:43:05 CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, ya kamata bangaren Japan ya yi taka tsan-tsan kan kalamai da ayyuka a fannonin soji da tsaro, da kara yin ayyukan da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Mao Ning ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na yau da kullum Talatar nan, lokacin da take amsa wata tambaya mai alaka da karuwar kasafin kudin tsaron kasar ta Japan.

Mao ta ce, kasafin kudin tsaron Japan ya karu cikin shekaru 10 a jere, sannan kuma kasar ta cika neman tayar da zaune tsaye a yankin da neman samun ci gaba a fannin soji, tana mai cewa, irin wannan mataki mai hadarin gaske ya haifar da shakku a tsakanin makwabtanta na yankin Asiya da kasashen duniya game da ko Japan za ta iya tsayawa kan manufar tsaro ta musamman da ma hanyar bunkasuwa cikin lumana.(Ibrahim)