logo

HAUSA

An yi hasashen karuwar tattalin arzikin UEMOA za ta kai 5.7% a bana

2022-12-06 14:06:11 CMG Hausa

Jiya Litinin an kira taron shugabannin kasashe mambobin kawancen tattalin arziki da kudi na kasashen yammacin nahiyar Afirka, wato UEMOA a takaice karo na 23 a birnin Abidjan, hedkwatar tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire, inda ministan tattalin arziki da harkokin kudi na kasar Togo, kuma shugaban zartaswa na taron ministocin kawancen UEMOA Sani Yaya ya yi tsokaci da cewa, an yi hasashen karuwar tattalin arzikin kasashen mambobin kawancen za ta kai kaso 5.7 bisa dari a bana.

Yaya ya kara da cewa, duk da cewa ana fuskantar tasirin rikicin Ukraine, da hauhawar farashin makamashi, da karuwar darajar dalar Amurka da sauransu, amma tattalin arzikin kasashen mambobin kawancen yana ci gaba da karuwa yadda ya kamata, sakamakon karuwar jarin da aka zuba, da ci gaban sana’o’in kere-kere da kasuwanci da kuma hidima.

Kana yaya ya ba da shawarar cewa, ya dace gwamnatocin kasashen su dauki matakai domin shawo kan raguwar darajar kudi, tare kuma da ingiza ci gaban kamfanoni masu zaman kansu. (Jamila)