logo

HAUSA

Ana kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Najeriya a yankin cinikayya cikin ‘yanci na Lekki

2022-12-06 15:10:46 CMG Hausa

Najeriya ce kasar da kasar Sin ke gudanar da manyan ayyukan gine-gine mafi yawa a nahiyar Afirka, kana kasar da Sin ke fitar da hajojinta mafi yawa a nahiyar. Har wa yau, dangantakar cinikayya na kara inganta tsakanin Sin da Najeriya a ‘yan shekarun nan, kuma akwai kamfanonin Sin da yawa dake matukar sha’awar zuba jari a Najeriya. A yankin Lekki dake kusa da birnin Lagos, wanda shi ne cibiyar tattalin arziki da kasuwanci ta Najeriya, akwai wani yankin gudanar da cinikayya cikin ‘yanci mai suna Lekki Free Trade Zone a turance, inda ake kara samun hadin-gwiwa tsakanin kasashen Sin da Najeriya.

Yankin cinikayya cikin ‘yanci na Lekki, yana da tazarar kilomita 60 da birnin Lagos dake kudu maso yammacin tarayyar Najeriya. An raba yankin, mai fadin murabba’in kilomita 165 gaba daya, cikin kananan yankuna hudu, ciki har da wani yanki mai fadin murabba’in kilomita 30, inda kamfanin raya yankin cinikayya cikin ‘yanci na Lekki mai suna Lekki Free Trade Zone Development Company ko kuma LFZDC dake karkashin jagorancin kamfanin kasar Sin ke gudanar da harkokinsa. Kawo yanzu, kamfanoni 76 ne suka rattaba hannu kan yarjeniyoyin zuba jari a wannan yanki, ciki har da guda 57 wadanda suka riga suka kafa ko suna kan gina masana’antun su a halin yanzu.

Kamfanin Colori cosmetics FZE, wani kamfanin kasar Sin ne dake samar da kayan kwalliya da sauran kayan masarufi a yankin cinikayya cikin ‘yanci na Lekki, kuma muhimmin kayan da kamfanin yake samarwa yanzu shi ne man goge baki. Ma’aikata ‘yan Najeriya da dama dake aiki a kamfanin, suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a kowace rana. Wani jami’in kamfanin Colori cosmetics FZE, Ao Tianjiao ya bayyana cewa:

“Muna da layukan samar da kayayyaki guda hudu a masana’antar mu, inda rukunonin ma’aikata biyu ke canjin aiki a kowace rana. Kowane rukuni yana kunshe da ma’aikata ‘yan Najeriya 85, inda ake samar da man goge baki dubu 300 a kowace rana. A nan gaba, za mu dauki hayar ma’aikata sama da 130 a kowane rukuni, wato adadin ma’aikatan rukunonin biyu zai kai 270 gaba daya, kana yawan dukkan ma’aikatan masana’antar mu zai zarce dari 5.”

Mary Mange, ma’aikaciya ‘yar Najeriya ce dake kula da ingancin kayayyakin da ake samarwa a kamfanin, inda ta bayyana cewa:

“Muna da dakunan gwaje-gwajen kimiyya daban-daban a masana’antar mu, inda muke gudanar da bincike kan kayayyaki da yawa. Kawo yanzu, komai na gudana yadda ya kamata. Babban aikin mu shi ne, tabbatar da ingancin kayayyakin da muke samarwa.”

A wata masana’antar samar da akwatunan takardu dake yankin cinikayya cikin ‘yanci na Lekki, wadda ke da fadin murabba’in mita dubu 10, ma’aikatan Najeriya na nuna himma da kwazo wajen gudanar da ayyukansu daban-daban. Daya daga cikin jami’an masana’antar, dan kasar Indiya ne mai suna Jenat Reddy ya bayyana cewa:

“Muna gudanar da ayyukan mu yadda ya kamata a halin yanzu, kuma akwai kyakkyawar mu’amala tsakanin sassa daban-daban. Gaskiya muna jin dadin aiki a nan. Duk wadannan na’urorin kamfanin, kirar kasar Sin ne, wadanda ke da inganci sosai. Ana kula da harkokin wannan yanki ba tare da matsala ba, ana kuma kara samun kamfanoni da suke aiki a nan. Muna yiwa wannan wuri kyakkyawan fata.”

A bangaren kudu maso gabashin yankin cinikayya cikin ‘yanci na Lekki, ana kokarin gina matatar mai ta kamfanin Dangote, wadda aka zuba kudaden da yawansu ya kai dala biliyan 19. Idan an kammala ta, za ta rika sarrafa albarkatun mai da yawansu ya kai ganga dubu 650 a kowace rana. Kamfanin kasar Sin ne yake daukar nauyin gina matatar man, kuma kawo yanzu an kusan kammala aikin. Li Guobiao, manaja ne mai kula da harkokin hada na’urorin matatar man, wanda ya bayyana cewa, tun da aka fara aikin gina matatar, zuwa yanzu an horas da ma’aikatan fasaha na wurin da yawansu ya zarce dubu 10. Li ya bayyana cewa:

“Kawo yanzu mun kammala kashi 97 bisa dari na dukkan ayyukan gina matatar mai na kamfanin Dangote. Tun farkon aikin ya zuwa yanzu, mun horas da ma’aikatan da adadin su ya zarce dubu 10, wadanda za su zama kwararru, idan gwamnatin Najeriya ta kara gudanar da irin wadannan ayyukan gine-gine a nan gaba. A halin yanzu akwai ma’aikata sama da dubu biyar a wajen. Mun dauki ma’aikata daga kasashe daban-daban a wajen wannan gagarumin aiki, ciki har da Bangladesh, da Pakistan, da Indiya, da Koriya ta Arewa, da China, da ma Najeriya. Wato mun yi kokarin hada kwararru daga kasashe daban-daban a waje guda, al’amarin da ya taimaka sosai ga aikin.”

Har wa yau, a gabar tekun Atilantika da babu nisa da matatar mai ta kamfanin Dangote, kamfanin China Habor Engineering Ltd, CHEC a takaice, ya mikawa gwamnatin kasar Najeriya Lekki, tashar teku mai zurfi ta farko ta kasar, bayan nasarar kammala katafaren aikin tashar jiragen ruwa da ya yi a Lagos, a ranar 31 ga watan Oktoba. Tashar teku mai zurfi da kamfanin CHEC ya gina, ita ce tashar ruwa mafi girma a Najeriya, kana daya daga cikin mafiya girma a yammacin nahiyar Afirka. An dai fara aikin gina tashar ce a watan Yunin shekara ta 2020, an kuma tsara tashar ta yadda za ta iya sarrafa kwantenoni miliyan 1.2 a shekara, da samar da guraban ayyukan yi ga mazauna wurin kimanin dubu 170.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa, sabuwar tashar jiragen ruwan, za ta sanya Lagos a matsayin cibiyar hada-hadar sufurin ruwan ba kawai a yammacin Afirka ba, har ma a yankin tsakiya da yammacin Afirka baki daya, al’amarin da zai kara sanya kuzari ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya, da kyautata rayuwar mazauna wurin, inda ya ce:

“Kamfanin CHEC ya kammala katafaren aikin gina tashar Lekki cikin lokaci kuma mai inganci, abun da ya zama aikin gina tashar ruwa mai zurfi ta zamani da na taba gani, kana alama ce ta jihar mu ta Lagos. Gaskiya muna alfahari sosai da wannan aikin, wanda kuma ya jawo mana jari sosai.” (Murtala Zhang)