logo

HAUSA

An fitar da rahoton masana kan ra’ayin kare hakkin dan Adam na Sin

2022-12-05 10:14:52 CMG Hausa

Yau Litinin, asusun raya aikin kare hakkin dan Adam na kasar Sin, da kungiyar manyan masanan kasar ta kamfanin dillancin labarai na Xinhua, sun fitar da rahoton masana mai taken “Domin tabbatar da dadin rayuwar al’ummar kasa: Kokarin da ake yi wajen cimma ra’ayin kare hakkin dan Adam a kasar Sin a zamanin yanzu” da harsunan Sinanci da Turanci.

Rahoton ya yi bayani kan babbar ma’ana, ta kokarin kare hakkin dan Adam da kasar Sin take yi, wajen ingiza aikin kyautata yanayin hakkin dan Adam da kasashen duniya ke ciki, da kuma ciyar da aikin kare hakkin dan Adam gaba daga dukkanin fannoni.

Ana iya bayyana ra’ayin kare hakkin dan Adam na kasar Sin kamar haka: “Hakkin dan Adam mafi girma shi ne tabbatar da jin dadin rayuwar al’ummar kasa”. Rahoton ya bayyana cewa, ya dace a nace kan manufar kiyaye moriyar al’ummar kasa, kuma sabbin matakan kare hakkin bil Adam da kasar Sin ta dauka sun samar da abin koyi ga sauran kasashen duniya, musamman ma ga kasashe masu tasowa.

Kana rahoton ya kara da cewa, ya dace a kara karfafa cudanya tsakanin wayewar kai mabambanta, ta yadda za a kyautata yanayin kare hakkin dan Adam da kasashen duniya ke ciki, da kuma kafa tsarin tafiyar da harkokin hakkin bil Adam na kasa da kasa mai adalci, tare kuma da gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya yadda ya kamata. (Jamila)