logo

HAUSA

Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 sun isa Beijing lafiya

2022-12-05 10:10:30 CMG Hausa

Rahotannin da ofishin kula da aikin nazarin sararin samaniya, da kumbo mai dauke da mutane na kasar Sin ya fitar sun nuna cewa, ‘yan sama jannatin da suka kammala aiki cikin kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou-14, wato Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe, sun sauka birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a asubar yau Litinin 5 ga wata lami lafiya, inda shugabanni da wakilai, na babbar hedkwatar kula da aikin gina tashar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin suka tarye su, a filin saukar jiragen sama.

Yanzu haka za a fara gwajin lafiyar ‘yan sama jannatin su uku daga dukkanin fannoni, ta yadda za su samu kulawar da suke bukata. (Jamila)