logo

HAUSA

Najeriya: ’Yan sanda sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su a Katsina  

2022-12-05 10:15:08 CMG Hausa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar ceto wasu mutane 6, cikin jimillar mutum 19 da masu garkuwa da mutane suka sace daga wani masallaci dake kauyen Maigamji a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Gambo Isah, ya ce ’yan bindiga sun aukawa masallacin ne a ranar Asabar, kuma sakamakon harbin bindiga da suka yi, sun jikkata masallatan 2.

Daga bisani ’yan bindigar sun tusa kyeyar masallatan su 19 zuwa daji. Sai dai jim kadan bayan faruwar al’amarin, ’yan sanda sun ceto mutum 2 tun a ranar Asabar, yayin da aka ceto karin mutane 4 a ranar Lahadi.

Gambo Isah, ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da baza komar su, domin gano tare da kubutar da ragowar mutane 13 da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su. (Saminu Alhasan)