logo

HAUSA

Sahihanci shi ne tushen hadin gwiwar Afirka da Sin

2022-12-05 14:53:28 CMG Hausa

Abokaina, ko kuna son cin Avacado? Kun san a nan kasar Sin ba a noma wannan nau’in ‘ya’yan marmari, saboda haka kusan ba wanda ya san shi kafin shekaru fiye da 10 da suka wuce.

Na tuna lokacin da na sayi Avacado a karon farko, ban san ya kamata a bari ya yi laushi ba kafin a ci shi. Sai na ci shi nan take bayan da na same shi, yayin da yake da tauri. Don haka ra’ayin da na samu game da Avacado a lokacin shi ne, wani nau’in ‘ya’yan marmari ne mai tsada, kuma maras dadi.

Tabbas daga bisani na san hanya mafi dacewa da ya kamata a bi wajen dandana Avacado. Kana saboda Sinawa sun kara fahimtar amfaninsa a fannin gina jiki, hakan ya sa ana shigo da karin Avacado cikin kasar Sin. Misali, a shekarar 2010, an shigo da Avacado ton 2 ne kacal cikin kasuwannin kasar Sin, amma zuwa shekarar 2018, wannan adadi ya karu zuwa ton 43,860, inda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 133.

Ban da wannan kuma, tun daga shekarar bana, kasar Sin ta fara shigo da Avavado daga wasu kasasahen Afirka, irinsu Kenya da Tanzania. Hakan na daga cikin matakan da aka dauka na cika alkawarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a wani taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wanda ya gudana a bara, wato “Ba da sauki ga shigowar amfanin gonan Afirka cikin kasuwar kasar Sin, kana da kokarin shigo da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 30 daga kasashen Afirka, cikin shekaru 3 dake tafe.”

Me ya sa kasar Sin ke neman shigo da karin kayayyaki daga nahiyar Afirka? Dalili shi ne, kasar Sin na neman daidaita cinikayyar da ake yi tsakaninta da kasashen Afirka.

Bayanan da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, ana samun daidaito tsakanin bangarorin Sin da Afirka ta fuskar ciniki. Sai dai idan an tantance bayanai game da daidaikun kasa dake nahiyar Afirka, za a ga wasu kasashe na fitar da dimbin kayayyaki zuwa kasar Sin, yayin da wasu ba su samun damar fitar da kayayyakinsu sosai. Saboda haka, don raba moriya ga wadannan kasashe, kasar Sin ta dauki matakin shigo da karin kayayyakinsu.

Matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka a shekarun nan, sun hada da gudanar da tarukan baje kolin kayayyakin Afirka a kasar Sin, da kafa cibiyoyin nuna kayayyakin Afirka a wasu biranen kasar, da shirya bukukuwan tallace-tallacen kayayyakin Afirka a dandalin sayar da kaya ta kafar yanar gizo ta Internet, da samar da rance ga wasu kamfanonin kasar Sin domin su shigo da karin kayayyaki daga kasashen Afirka, da dai sauransu. Kana sabbin matakan da kasar Sin ta dauka a bana, sun hada da fara shigo da Avacado daga kasashen Afirka, da yafe wa karin wasu kasashe mafi rashin karfin tattalin arziki harajin da ake karba bisa kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasar Sin, wadannan kasashe sun hada da Benin, da Burkina Faso, da Guinea Bissau, da Lesotho, da Malawi, da Sau Tome da Principe, da Tanzania, da Uganda, gami da Zambia.

Wadannan matakai sun nuna yadda kasar Sin take da sahihanci, yayin da take hadin gwiwa tare da kasashen Afirka. Idan ana son kulla huldar hadin kai mai dorewa, dole ne a kulla huldar cin gajiyar juna. Sai dai ta yaya za a iya tabbatar da hakan? Amsa ita ce ta yin mu’ammala cikin daidaito, da daidaita matakai akai akai, ta yadda za a iya tabbatar da daidaituwar moriyar bangarori daban daban, da sanya kowa ya gamsu.

Wannan ma dalili ne da ya sa kasashen Afirka, ba sa amincewa da wasu maganganu marasa kyau da wasu kasashe suka fada, game da huldar hadin gwiwar Afirka da Sin. Kasashen Afirka sun ga sahihancin da kasar Sin ta nuna, kuma sun san duk wata matsalar da aka samu, yayin da ake hadin kai da kasar Sin, za a iya warware ta ta hanyar mu’ammala, da daidaita manufofi. Saboda haka, ba su damuwa game da huldar hadin kai da suka kulla tare da kasar ta Sin. (Bello Wang)