logo

HAUSA

Sin ta sauke nauyin dake wuyanta wajen taimakawa kasashen da suka fi rashin ci gaba

2022-12-05 19:58:22 CMG HAUSA

DAGA MINA

Daga ran 1 ga wata, kasar Sin ta cire haraji kan kaso 98 cikin 100 na nau’o’in kayayyakin da take shigo da su daga wasu kasashen da suka fi rashin samun ci gaba guda 10, ciki hadda Benin da Burkina Faso da Guinea Bissau da Tanzaniya da Uganda da Zambiya da sauransu. Kawo yanzu dai, gaba daya kasashe 26 na amfana da wannan manufa. Yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku wannan manufa mai kyau da ma yadda Sin ta sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa kasashen da suka fi rashin samun ci gaba.

Wannan manufa ta baiwa kasashen damar fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwar kasar Sin mai girma ba tare da biyan haraji ba. A hakika, tun daga shekarar 2008, Sin ta yi ta kara kayayyaki da kasashen da za su amfana da wannan manufa.

Ya zuwa yanzu, kasashe 26 da suka kulla yarjejeniyar rashin biyan haraji kan kayayyaki na kaso 98 cikin 100 da za su shigar Sin, 18 daga cikinsu kasashen Afrika ne. Alkaluma na nuna cewa, yawan kudin dake shafar ciniki tsakanin Sin da Afrika a shekarar 2021 ya karu da kashi 25.3% bisa na makamancin lokaci na 2020, daga cikinsu darajar yawan kayayyakin Afirka da suka shiga kasuwar Sin ya kai dala biliyan 105.9, wanda ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Yadda kasashen suke iya fitar da kayayyakinsu kasuwar kasar Sin ba tare da biyan kudin haraji ba, ya taimakawa al’ummar wadannan kasashe wajen samun aikin yi da jawo jarin waje a wasu sha’anoni da ma ingiza samun bunkasuwa cikin daidaito da sauransu.

Masu iya magana na cewa, ka so wa dan uwanka abin da ka so wa kanka. Sin ta dade tana sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa kasashen da suka fi rashin samun ci gaba a duniya, da kara ba su damar fitar da kayayyakinsu kasuwannin kasar Sin. Abin dake da muhimmiyar ma’ana ga hadin kansu a fannin kawar da talauci da cin moriyar juna da more kyakkyawar makoma tare.

An yi imanin cewa, hadin kan Sin da Afrika zai amfanawa al’umomin bangarorin biyu. Sin tana kokarin cika alkawarinta na taimakawa kasashe da suka fi rashin samun ci gaba, matakin dake bayyana niyyar Sin a bangaren samun bunkasuwa tare da rungumar kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da sauran kasashe. (Mai zane da rubuta: MINA)