logo

HAUSA

IMF ya yaba da yadda tattalin arzikin Seychelles ya farfado sosai

2022-12-04 17:42:28 CMG HAUSA

 

Assusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi maraba da farfadowar tattalin arzikin kasar Seychelles da karfin gaske.

Wannan na zuwa ne, bayan da hukumar gudanarwar asusun na IMF, ta kammala nazari a karo na uku a ranar Alhamis din da ta gabata, kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana, wanda ya bai wa tsibirin damar tsara samun rance a karkashin asusun neman agaji na tsawon watanni 32 (EFF).

Asusun IMF ya bayyana a cikin wani rahoto cewa, tattalin arzikin kasar ya farfado matuka a shekarar 2022, sakamakon sake farfado da fannin yawon bude ido da sauri fiye da yadda ake tsammani.

Ya zuwa karshen watan Satumban shekarar 2022, masu zuwa yawon shakatawa, sun karu da kashi 125 cikin 100, idan aka kwatanta da makamancin lokacin na shekarar 2021 sosai fiye da yadda ake tsammani daga Turai da yankin Gabas ta Tsakiya.

Asusun ya kara da cewa, farfadowar ta kasance tare da managarcin tsarin kasafin kudi gami da tallafin zamantakewa ga wadanda ke da rauni.(Ibrahim)