logo

HAUSA

Turai ta san ra’ayin Amurka kan dangantakar dake tsakaninsu

2022-12-04 17:18:05 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gama ziyararsa ta kwanaki 3 a kasar Amurka. Shugaba Macron ya ziyarci Amurka a wannan karo don sa kaimi ga kasar Amurka da ta gyara dokar rage hauhawar farashin kaya bisa la’akari da kamfanonin Turai. Amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, inda ya koma Turai ta bacin rai, duk da dangantakar dake tsakanin Turai da Amurkar.

Shugaba Macron ya ziyarci Amurka a wannan karo don neman dawo da moriyar Turai. A watan Agusta na bana, shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya sa hannu kan dokar rage hauhawar farashin kaya, inda aka gabatar da matakai da dama, ciki har da samar da kudin rangwame don sa kaimi ga kamfanonin da ke kasar Amurka da su raya fasahohin kera motoci masu amfani da wutar lantarki da sauran fasahohi ba tare da gurbata muhalli ba. Kasashen Turai sun nuna rashin jin dadi da wannan doka, domin a ganinsu, dokar tana kunshe da abubuwan bada kariya ga cinikayya, wadda ta sabawa ka’idojin hukumar WTO, kuma hakan zai tsananta halin da masana’antun samar da kaya na Turai ke game da game da kokarinsu na samar da kayayyaki, da tilastawa rassan kamfanonin Turai kaura zuwa kasar Amurka.

Yayin da shugaba Macron ya isa kasar Amurka a yini na farko, ya fara zargin babbar illar da dokar rage hauhawar farashin kaya ta Amurka ta haifar wa kamfanonin Turai, ya ce za a rasa ayyukan yi da dama a kasar Faransa da ma nahiyar Turai, kuma an dauki matakin ne don daidaita matsalar Amurka tare da kawo illa ga moriyar Turai. Shugaba Macron ya kara da cewa, kasar Faransa tana fatan kasar Amurka za ta dauki Faransa a matsayin abokiya, tare da kara yin mu’amala da juna kan tattalin arziki a tsakanin gabobin tekun Atlantic.

Game da bukatun da shugaba Macron ya gabatar, shugaba Biden ya ce kasar Amurka ba ta bukatar yin afuwa ga nahiyar Turai, Amurka za ta dan yiwa dokar gyara ne, amma bai yi karin haske ba. Kafofin watsa labarai na kasar Jamus sun bayyana cewa, game da batun moriyar tattalin arziki, kasar Amurka tana kula da moriyarta ce kawai, don haka ya kamata kasashen Turai su san da haka. (Zainab)