logo

HAUSA

Huang Keying: Cibiyar koyar da ilmin sana’a ta Luban dandamali ne mai kyau na sada zumunci a tsakanin Thailand da Sin

2022-12-05 19:59:44 CMG Hausa

Huang Keying, 'yar kasar Thailand, malama ce a Kwalejin koyon sana’o’i na Bohai na birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, tana koyar da daliban Thailand harshen Sinanci. Huang Keying ta ce, yayin da take rayuwa da aiki a kasar Sin, ta sha shaida ake zurfafa mu’amala a fannonin kasuwanci da tattalin arziki da ma'aikata tsakanin Thailand da Sin. A nan gaba tana fatan zama wata gadar kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.

“Assalamu alaikum, sunana NITINUN CHOMCHUEN, sunana na Sinanci Huang Keying, ni ‘yar kasar Thailand ce, kuma na yi shekaru takwas a kasar Sin. A halin yanzu ina aiki a Kwalejin koyon sana’o’i na Bohai dake birnin Tianjin.”

Huang Keying ta fito ne daga lardin Nonthaburi na kasar Thailand. Idan aka kwatanta da garinsu, wanda yake da dumi da sanyi tsawon shekara, Tianjin, mai yanayi daban-daban guda hudu, ya sa Huang Keying ba ta ji dadi ba a karon farko da ta iso birnin. Amma duk da haka, ta fara sha’awar rayuwa a birnin. Ta ce,

“Kasar Sin da na ji labarinta ina ‘yar shekaru bakwai ko takwas ba daidai ba ne da abin da na gani da idona. Kasar Sin tana da ci gaba sosai, kuma mutanen Tianjin suna da kirki da son baki. Har ila yau, kayayyakin more rayuwa na kasar Sin sun samu kyautatuwa sosai. Alal misali, farashin tikitin motocin bas ko jiragen karkashin kasa na da sauki da kuma araha, wannan na daga cikin managartan manufofin gwamnatin kasar Sin game da inganta jin adin rayuwar jama’a. Haka kuma akwai wuraren shakatawa na zamani da yawa.”

Bayan da ta shafe tsawon shekaru 8 tana zaune a kasar Sin, Huang Keying ta riga ta iya yaren Sinanci sosai, sakamakon kwazon ta tun tana makarantar sakandare. Saboda tana sha’awar al'adun kasar Sin, shi ya sa ta zabi karanta Sinanci a Jami'ar Fasaha ta Thailand a digiri na farko. Huang Keying ta kara da cewa, idan aka kwatanta da lokacin baya, yanzu haka ana samun karin matasan kasar Thailand da ke soma koyon Sinanci da sha'awar al'adun kasar Sin.

“Yanzu ‘yan Thailand dake koyon Sinanci na karuwa. Yadda ake kafa azuzuwan koyon Sinanci a manyan makarantun sakandare a kasar Thailand ya zama ruwan dare, su ma makarantun sakandare da na firamaren kasar, sun fara koyar da Sinanci. Abokaina da yawa a Thailand, suna kallon shirye-shiryen talabijin da fina-finai na kasar Sin sosai.”

A shekarar 2014, saboda kyakkyawan sakamakon da ta samu a karatunta, Huang Keying ta samu gurbin karatu daga gwamnatin kasar Sin, abin da ya ba ta damar zuwa jami'ar Tianjin don yin karatun digiri na biyu. Bayan kammala karatunta, ta je kwalejin koyon sana’o’i na Bohai na birnin Tianjin don yin aiki, inda ta sadu da Cibiyar koyar da ilmin sana’a ta Luban, wadda ta yi suna sosai wajen koyar da sana’o’i a kasar Sin.

A shekarar 2016, kwalejin koyon sana’o’i na Bohai na birnin Tianjin ya kafa Cibiyar koyar da ilmin sana’a ta Luban, wadda ta kasance irinta ta farko da kasar Sin ta kafa a kasashen ketare. Bisa ingantuwar shawarar “Ziri daya da hanya daya” aka soma kafa cibiyoyin koyar da ilmin sana’a ta Luban a kasashen ketare, da kafa wani tsarin kasa da kasa na ba da illmin sana’a, wanda ya kunshi dukkan matakai daga sakandare zuwa jami’a, daga ba da horo a fannin sana’o’in hannu zuwa karatun digiri na farko.

Yanzu, baya ga koyar da Sinanci ga daliban kasashen waje, Huang Keying tana kuma kula da ayyukan cudanya na cibiyar ta Luban a Thailand, da horar da malamai da dalibai na gajeren lokaci tsakanin Sin da Thailand, da shirye-shiryen horar da dalibai na Sin da Thailand na dogon lokaci da dai sauransu.

Huang Keying ta ce, kasar Sin ta yi fice a fannin ba da ilmin sana'o'in hannu, wannan ya sa daliban kasar Thailand da suka yi karatu a cibiyar Luban, samun aikin yi cikin sauki.

“Za a baiwa daliban da suka kammala karatunsu a kasashen Thailand da Sin, takaddun shaida, kuma hakan zai taimaka musu wajen samun aikin yi. Baya ga fasahar da suka koya daga kasar Sin sun kuma fahimci al'adun Sinawa, da iya magana da Sinanci, don haka suna iya samun aiki cikin sauki, kuma mai yiwuwa ma da albashi mai kyau.”

A ganin Huang Keying, cibiyar koyar da ilmin sana’a ta Luban, ba wai kawai ta hada da ayyukan ba da ilmi a fannin sana'o'i a tsakanin kasashen Thailand da Sin ba, har ma ta taimaka wajen raya tattalin arziki da zamantakewar kasashen biyu, da horar da kwararrun ma'aikata, tare kuma da yin tasiri mai kyau ga wasu kasashen kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN da dama.

“A ganina, cibiyar Luban wani dandamali ne mai kyau, wasu daliban wasu kasashe, ciki har da Indonesiya da Malaysia da sauransu sun iya ziyarta da samun horo a cibiyar dake kasar Thailand.”

Huang Keying ta ce tun tana karama ta ji iyayenta na cewa "Sin da Thailand ‘yan uwan juna ne". Yanzu, tana da iyali da sana'a a birnin Tianjin na kasar Sin, kuma tana kokarin cimma burinta ta hanyar dandalin cibiyar Luban. Tana fatan ci gaba da ba da gudummawarta wajen sada zumunta tsakanin Thailand da Sin. Ta ce,

“Ni ba kowa ba ce, ina fatan zama gada tsakanin Sin da Thailand, don inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ina fatan kokarin da nake yi, za ta kara zumuncin dake tsakanin al’ummomin Thailand da Sin.”