logo

HAUSA

AU da MDD sun kaddamar da asusun neman taimako na dalar Amurka biliyan 51.5

2022-12-03 17:09:32 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da hadin gwiwar ofishin tsare tsaren ayyukan jin kai na MDD ko UNOCHA, sun kaddamar da wani asusun neman taimako, domin ayyukan da ake fatan gudanarwa a shekarar 2023, wanda karkashinsa ake fatan tara kudaden da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 51.5, na tallafawa mutane da yawan su ya kai miliyan 230, dake cikin mawuyacin hali a sassa daban daban na duniya.

Wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, ta ce hukumar zartaswar AU, da hadin gwiwar ofishin UNOCHA, sun kuma kaddamar da rahoton alkaluman bukatun jin kai na duniya na 2023, a helkwatar AU dake birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.

Kungiyar AU ta ce rahoton GHO-2023, ya fayyace alkaluman bukatun jin kai, wadanda suka nuna cewa, adadin mutane dake neman taimakon kare rayuwa, da masu neman mafaka a kasashen duniya 68, ya kai mutum miliyan 339. Kaza lika, daya cikin duk mutane 23 dake rayuwa a duniya, na bukatar agajin gaggawa domin su rayu.

Bugu da kari, a cikin wadannan alkaluma, mutane miliyan 145 na rayuwa ne nahiyar Afirka. Don haka rahoton na GHO-2023, ya yi kira da a tattara kudaden da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 51.5, domin samar da agaji ga mafiya bukata su miliyan 230, dake rayuwa a sassan duniya daban daban. (Saminu Alhassan)