logo

HAUSA

Rukunoni biyu na ‘yan sama jannatin kasar Sin sun yi musayar aiki a tashar binciken samaniya ta Sin

2022-12-03 17:05:02 CMG Hausa

Hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin ko CMSA a takaice, ta ce ‘yan sama jannati 3, da suka isa tashar samaniya ta kasar Sin ta kumbon Shenzhou-15, sun yi musayar kama aiki irinta ta farko da rukunin ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 a jiya Juma’a.

A ranar Laraba ne ‘yan sama jannatin Shenzhou-15, suka shiga tashar binciken samaniya ta Sin, inda suka hadu da takwarorin su na kumbon Shenzhou-14, wadanda ke aiki a tashar tun cikin wata Yuni. Haduwar rukunonin ‘yan sama jannatin 2, ta kafa tarihin samun karin ‘yan sama jannati zuwa mutum 6, wadanda a karon farko suka yi hadakar gudanar da ayyuka a cikin dakin gwaje gwaje dake tashar.

Yanzu haka dai tasahar samaniya ta Sin ta shiga wani lokaci na zaman 'yan sama jannati na tsawon lokaci.

Har ila yau, hukumar CMSA ta ce ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14, sun kawo karshen dukkanin ayyukan da ya dace su gudanar a tashar samaniya ta Sin, kuma za su dawo doron duniya a ranar Lahadi. Bugu da kari, hukumar ta ce tun a daren ranar Alhamis, tawagar masu bincike da ceto da aka tanada, ta kammala gwajin aiki, domin tabbatar da gano wurin saukar ‘yan sama jannatin dake shirin dawowa doron duniya.   (Saminu Alhassan)