logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe masu tsattsauran ra’ayi a kalla 11 a cikin makonni biyu

2022-12-02 11:12:16 CMG Hausa

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Musa Danmadami, ya bayyana cewa, a kalla mayakan tsageru masu tsattsauran ra’ayi 11 ne aka kashe a farmakin da dakarun gwamnatin Najeriya suka kaddamar, a yankin arewa maso gabashin kasar cikin makonni biyu da suka gabata

Musa Danmadami ya bayyana haka ne jiya Alhamis, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce da yawa daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram da ISWAP, su ma sun tsere da raunukan harbin bindiga, a wasu samame daban-daban da sojojin suka kaddamar a yankin jihohin Borno da Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar daga ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba.
Ya kara da cewa, farmakin sojojin, ya kai ga kubutar da wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su daga maboyar ‘yan ta’addan, tare da kame a kalla ‘yan bindiga 47 da masu taimaka musu.
Jami’in ya ce, a ranar 20 ga watan Nuwamba, yayin daya daga cikin irin wadannan kwanton bauna da samame da aka kaddamar, sojojin kasar sun yi nasarar damke wani kasurgumin mai samarwa ‘yan Boko Haram da ISWAP kayayyaki, a wani shingen binciken sojoji da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno da ke yankin arewacin kasar. (Ibrahim)