logo

HAUSA

Layin dogo na Sin zuwa Laos ya samu bunkasuwa cikin shekara guda da bude shi

2022-12-02 20:56:41 CMG Hausa

Ya zuwa yau Juma’a, fasinjoji sun yi zirga zirgar da ta kai sama da miliyan 8.5, kan layin dogo na Sin zuwa Laos, yayin da kuma adadin hajoji da aka yi dakon su ta layin dogon ya kai tan miliyan 11.2, tun bayan bude layin shekara guda da ta gabata.

A cewar kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin, layin dogon na Sin zuwa Laos, ya samar da hanya mai inganci da sauki ta zirga zirga tsakanin kasashen 2, tare da taimakawa wajen gudanar da hidimomin aikewa da hajoji tsakanin Sin da mambobin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya.

Layin dogon ya hade birnin Kunming na lardin Yunnan na kasar Sin da Vientiane fadar mulkin kasar ta Laos. A ranar 3 ga watan Disambar bara ne aka kaddamar da fara aiki da layin dogon mai inganci, wanda ke da tsayin kilomita 1,035, wanda kuma aka gina karkashin hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya.  (Saminu Alhassan)