logo

HAUSA

Shugabannin Afirka sun himmatu wajen habaka masana'antun nahiyar

2022-12-02 10:41:51 CMG Hausa

Shugabannin kasashen Afirka, sun kuduri aniyar cimma matsaya tare da tsai da kuduri, don zamanantar da masana'antu gami da fadada tattalin arziki da cinikayya a nahiyar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta fitar a jiya Alhamis, ta bayyana cewa, yayin taron kolin kungiyar kan bunkasa masana'antu da habaka tattalin arziki da aka gudanar a makon da ya gabata a jamhuriyar Nijar, shugabannin sun sake nanata bukatar raya masana'antu da fadada sassan tattalin arzikin nahiyar, tare da ba da fifiko kan kiwon lafiya da magunguna, da motoci, da ma'adanai, da abinci mai gina jiki, da tufafin da masana'antun auduga ke samarwa domin rage dogaro da nahiyar ke yi daga waje.

Sanarwar ta bayyana cewa, shugabnnin sun kuma jaddada bukatar kara zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa, da makamashi, tare da tallafin cibiyoyin kudi da abokan hulda, don rage kudaden da ake kashewa wajen samar da kayayyaki, da kuma kara karfin tattalin arzikin kasashen nahiyar.

Bugu da kari, sun amince da samar da kafa yankunan tattalin arziki na musamman da rukunonin masana'antu, tare da agazawa wadanda ake da su.(Ibrahim)