logo

HAUSA

Kasar Sin na fatan Amurka za ta aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma

2022-12-02 19:31:56 CMG Hausa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya sake yada kalaman bata sunan kasar Sin. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, kalaman Blinken sun jirkita gaskiya, kuma cike suke da ra’ayin yakin cacar baka da nuna bambanci.

Rahotannin da aka ruwaito sun ce a ranar 30 ga watan Nuwamba, bayan taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar NATO, Blinken ya fadawa manema labarai cewa, NATO din a shirye take, ta tinkari kalubalen kasar Sin, kana Amurka tana maida hankali sosai kan manufofin kasar Sin na tilastawa sauran kasashe yin wani abu, da yadda take yada bayanan karya.

Game da wannan furuci nasa, Zhao Lijian ya jaddada cewa, Amurka ita ce ta fara aiwatar da manufofin diflomasiyya dake tilastawa sauran kasashe yin wani abu, ciki har da kawo barazana ta fuskar aikin soja, da nuna wariya a fannin siyasa, da kuma sanya takunkumi a fannonin tattalin arziki da fasahohi, laifukan da duk Amurka ta aikata su. Har wa yau, adadin bayanan karya da Amurka take yayatawa, ba sa misaltuwa.

Zhao ya sake nanata cewa, kasar Sin tana tsayawa haikan, kan manufofin diflomasiyya masu zaman kansu, dake goyon-bayan zaman lafiya, kuma ba ta taba tilasta wa sauran kasashe, ko yada bayanan karya ba. Ya dace Amurka ta dakatar da shafawa kasar Sin bakin fenti, saboda ana bukatar kokarin kasashen biyu, wajen tabbatar da kyakkyawar alakar su yadda ya kamata. (Murtala Zhang)