logo

HAUSA

Najeriya: Za a dawo da zirga zirgar jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna

2022-12-02 21:31:30 CMG Hausa

Hukumar dake lura da sufurin jiragen kasa ta tarayyar Najeriya, ta sanar da cewa, daga farkon mako mai zuwa, za a dawo da zirga zirgar jiragen kasa tsakanin birnin Abuja zuwa Kaduna, bayan dakatar da hakan na tsawon watanni 8, sakamakon harin da aka kaiwa wani jirgin kasa dake bin hanyar a karshen watan Maris.

Da yake tabbatar da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis a Abuja fadar mulkin kasar, babban manajan daraktan hukumar Fidet Okhiria, ya ce fasinjojin dake son bin jirgin kasan za su iya sayen tikiti nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Mr. Okhiria ya kara da cewa, an dauki kwararan matakan tsaro, domin baiwa fasinjojin da za su rika hawa jirgin kasar cikakken tsaro. (Saminu Alhassan)