logo

HAUSA

An yi atisayen karshe na dukkan fannoni don share fagen karbar kumbon Shenzhou-14

2022-12-02 21:13:05 CMG Hausa

Da daren jiya Alhamis 1 ga wata ne aka gudanar da atisayen karshe daga dukkan fannoni, don share-fagen karbar kumbon Shenzhou-14. Kawo yanzu, an shirya tsaf don maraba da dawowar kumbon duniyar mu.

Bisa shirin da aka tsara, bayan da ‘yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-14, suka mika ayyukansu ga takwarorin su dake cikin kumbon Shenzhou-15, za su dawo doron duniyar nan ba da jimawa ba. (Murtala Zhang)