Labarai masu dumi-dumi a gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa ta shekarar 2022
2022-12-01 13:29:27 CRI
Qatar 2022: Messi ya ceci Argentina kuma Mbappe ya taimaki Faransa shiga kungiyoyin 16 da za su buga zagaye na 2
Yayin da ake ci gaba da buga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya yanzu haka a kasar Qatar, tauraron dan kwallon Argentina Lionel Messi, ya ci wa kungiyarsa kwallo daya, a wasan da ta doke Mexico da ci 2 da nema. Kaza lika a daya wasan da aka buga a ranar 26 ga watan jiya, Kylian Mbappe ya ci kwallaye biyu, a wasan da Faransa ta buga da Denmark, inda aka tashi Faransa na da kwallo 2 Denmark na da 1. Da wannan sakamako, Faransa ta samu gurbin buga zagaye na biyu na gasar mai kunshe da kungiyoyi 16.
Har ila yau a dai a ranar 28 ga watan da ya gabata, Poland ta doke Saudiyya da ci 2 da nema.
A daya wasan kuma tsakanin Australia da Tunisia, Australia ce ta yi nasara da ci 1 da nema, kuma da wannan sakamako, Australia za ta buga wasan ta na gaba da Denmark.
Serbia da Kamaru sun ci gaba da nuna fatan fafatawa a gasar cin kofin duniya na Qatar
Kungiyoyin wasa na kasashen Serbia da Kamaru, sun fuskanci matsin lamba, wajen farke kwallayen da aka zura musu a fafatawar rukuni na G a ranar 28 ga watan da ya gabata, inda suka ci gaba da nuna fatan shiga zagayen kasashe 16 da za su fafata a zagayen gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar.
Jean-Charles Castelletto ne ya fara zura kwallo a ragar Serbia, a mituna na 29 da fara wasa, abin da ya baiwa kasarsa kwallon farko, a bugun kusurwa daga bangaren hagu da suka samu.
Serbia ta sauya wasan, bayan kwallaye biyun da ta zura a ragar Kamaru a cikin karin lokaci kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Sai dai cikin mituna 8 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Aleksandar Mitrovic, ya jefa kwallo ta uku a ragar kamaru, inda wasa ya zama ci 3 da 1.
Kamaru, wadda ke neman nasara ta farko a gasar, tun shekarar 2002, ta matsa kaimi, inda Vincent Aboubakar ya jefa kwallo ta biyu a ragar Serbia a mituna na 63, daga bisani kuma Choupo-Moting ya zura tasa kwallon bayan mintuna uku.
Shugaban Ghana ya jinjinawa ‘yan wasan Black Stars kan yadda suka doke Koriya ta kudu
Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana, ya taya tawagar Black Stars ta kasar murnar doke Koriya ta kudu a gasar wasan cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a Qatar.
Akufo-Addo ya fada a shafinsa na Tiwita cewa, ‘yan wasan sun cancanci wannan nasara. Yana mai cewa, “Ina yabawa ‘yan wasan Black Stars. An barje gumi, amma kun cancaci nasarar da kuka yi a kan Koriya ta kudu. Ina alfahari da baki dayan tawagar da ma goyon bayan da al’ummar Ghana suka ba su”.
Shugaban ya kuma bukaci kungiyar, da ta mayar da hankali kan wasan karshe na rukinin H da za su fafata da Uruguay ranar Jumma’a. Yana mai cewa, “Za mu yi nasara”.
Mohammed Kudus ne, ya zura kwallaye biyu da ya baiwa Ghana nasara a wasan da suka doke Koriya ta kudu a ranar 28 ga watan da ya gabata da ci 3 da 2.
An samu hatsaniya a Brussels bayan da Belgium ta yi rashin nasara a wasa mai mahimmanci a Qatar
'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla, bayan da magoya bayan kwallon kafa suka kai musu hari a tsakiyar Brussels a ranar 27 ga watan da ya gabata, bayan da kasar Morocco ta lallasa Belgium da ci 2-0 a gasar cin kofin duniya dake gudana a Qatar.
Magoya baya da dama sun farfasa tagogin kantuna, tare da jefa kayan wuta da kona motoci.
Tun kafin a kammala wasan, jama'a da dama, ciki har da wadanda suka rufe fuskokinsu, sun nemi yin arangama da ‘yan sanda, lamarin da ya yi illa ga tsaron jama’a, kamar yadda ‘yan sandan Brussels din suka bayyana a cikin wata sanarwa.
Mai magana da yawun 'yan sandan ta ce, wasu magoya bayan na dauke da sanduna, haka wani dan jarida ya ji rauni a fuska sanadiyar wasan wuta".
Morocco ta doke Belgium a gasar cin kofin duniya karo na farko cikin shekaru 24
A ranar 27 ga watan da ya gabata ne, kasar Morocco ta fita kunya a gasar cin kofin duniya, bayan da kungiyar kwallon kafan ta Afrika, ta yi nasara a kan Belgium a karon farko cikin shekaru 24, bayan ta doke ta da ci 2-0.
Nasara ta karshe da Moroccon ta yi a gasar cin kofin duniya, ita ce a shekarar 1998, inda ta lallasa Scotland da ci 3-0, abin da ya sanya ficewa daga gasar.
Wannan dai shi ne karo na uku da Morocco ta samu nasara a tarihin gasar cin kofin duniya, inda ta samu nasara ta farko a shekarar 1986, bayan da ta doke Portugal da ci 3-1.
Morocco ta jefa kwallonta na fako a minti na 73 da fara wasan, yayin da dan wasan tsakiyar kulob din Sampdoria na Seria A Abdelhamid Sabiri ya murza kwallon a ragar mai tsaron gidan Belgium wato Thibaut Courtois Zakaria Aboukhlal, wanda ya shigo wasan daga baya, ya baiwa Morocco nasara mai kayatarwa a minti na 92 da fara wasa. Yanzu dai Morocco ce ke kan gaba a rukunin F da maki hudu a gaban Belgium, kafin wasan karshe na rukuni tsakanin Canada da Croatia.
Morocco za ta kara da Canada yayin da ita kuma Belgium za ta baje gumi da Croatia a ranar Alhamis a wasan karshe na rukuni.
Senegal ta samu damar kaiwa ga zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya na Qatar
A ranar 29 ga watan da ya gabata ne, kasar Senegal ta yi nasarar doke Ecuador, a gasar cin kofin duniya dake gudana yanzu haka a kasar Qatar. ’Yan wasan Senegal Isma’ila Sarr da Kalidou Koulibaly ne suka jefawa kasarsu kwallaye a ragar Ecuador, kuma karon farko cikin shekaru 20 da kasar ta samu damar kaiwa mataki na kifuwa daya kwale na gasar. An dai tashi wasan a ranar 29 ga watan da ya gabata ne, ci biyu da 1.