logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi shawarwari da shugaban majalisar zartaswar Turai

2022-12-01 16:02:46 CMG Hausa

A safiyar yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar zartaswa ta Turai Charles Michel a babban dakin taruwar jama'a da ke birnin Beijing.

Xi Jinping ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai ta dade da ci gaba, wadda ta dace da muradun bangarorin biyu da na kasashen duniya. Game da ci gaban dangantakar, Xi ya gabatar da ra’ayoyi guda hudu, na farko shi ne tabbatar da sanin juna yadda ya kamata, na biyu shi ne warware sabane-sabane yadda ya kamata, na uku shi ne inganta hadin kansu, sai na hudu kyautata daidaituwa a tsakanin kasa da kasa.

A jawabinsa Michel ya nuna cewa, Tarayyar Turai tana fatan zama abokiyar hadin gwiwar Sin ta kwarai.

A yayin tattaunawar bangarorin biyu kan matsalar Ukraine, Xi ya bayyana matsayin kasar Sin, yana mai cewa, warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa na dacewa da moriyar kasashen Asiya da Turai.(Safiyah Ma)