logo

HAUSA

Sin ta bukaci kasashen duniya da su yi aiki tare don warware batun Falasdinu

2022-12-01 15:13:07 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang,ya gabatar da jawabi yayin babban taron MDD game da batun Falasdinu da yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya a jiya Laraba, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki tare don warware batun Falasdinu cikin adalci daga dukkan fannoni.

Geng Shuang ya ce, batun Falasdinu shi ne tushen batun yankin gabas ta tsakiya. Yadda za a warware matsalar Falasdinu cikin adalci daga dukkan fannoni, zai shafi batun samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da kuma batun samun adalci a kasa da kasa.

Tun farkon shekarar bana, yanayin da ake ciki a yankin falasdinawa da aka mamaye na ci gaba da tabarbarewa. Hakikanin abu ya sake shaida cewa, matakan shawo kan rikice-rikice da ake dauka yanzu ba za su iya maye gurbin shirin warware batun Falasdinu cikin adalci daga dukkan fannoni ba, kuma ba za a iya warware matsalar siyasa da tsaro da aka dade ana fuskanta a yankin ba ta hanyar samar da taimakon tattalin arziki da na jin kai kawai. Abin da ake bukata a halin da ake ciki yanzu, shi ne tsayayyen kudiri a siyasance da daukar kwararan matakan diflomasiyya, wadanda suka hada da kokarin kwamitin sulhu na MDD da dukkan kasashen duniya.

Geng Shuang ya kara da cewa, Sin ita ce aminiyar al’ummar Falasdinu, wadda ke goyon bayan samun zaman lafiya a tsakanin Falasdinu da Isra’ila. A kan batun Falasdinu, ko da yaushe Sin na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da samun zaman lafiya da adalci. Haka zakila ma dai, Sin na kara kwarin gwiwar Falasdinu da Isra’ila wajen tabbatar da tsaro tare. Falasdinu da Isra’ila makwabtan juna ne da ba za a iya raba su ba, wadanda ke dogaro da juna a kan batun tsaron kansu. Zai yi wahala a fita daga rudanin tsaro, idan har aka gina tsaron bangare daya ba tare da gyara na bangare dayan ba. Ya kamata kasa da kasa su mai da hankali kan matsalolin tsaron bangarorin biyu, karfafa gwiwarsu wajen cimma daidaito a tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da hadin kai, a kokarin tabbatar da tsaro a tsakaninsu.(Safiyah Ma)