logo

HAUSA

Hadin gwiwa tsakanin matasan Sin da Afirka zai fadada cin gajiyar kasashen su

2022-12-01 17:12:27 CMG Hausa

Bayan kammalar dandalin matasan Sin da Afirka karo na biyu da aka gudanar a ‘yan kwanakin baya ta kafar bidiyo, masana da masu fashin baki sun nuna gamsuwa da ma’anar dandalin, bisa yadda aka yi amfani da shi wajen yin kira da a karfafa kawance, da hadin gwiwa a fannoni daban daban, domin raya Sin da Afirka bisa juriya da cin moriyar juna yadda ya kamata.

Dandalin wanda kungiyar sada zumunta tsakanin jama’ar kasar Sin da ta kasashen waje ko CPAFFC ta shirya, ya hallara masu ruwa da tsaki a fannin tsara manufofi, da ma’aikatan diflomasiyya, da masana, da dalibai, da wakilai daga kungiyoyin lura da walwalar jama’a, ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwa tsakanin matasan Sin da na kasashen Afirka, a matsayin wani ginshiki na kyautata rayuwar bil adama. Wanda kuma nasarar sa za ta bude wani sabon babin goyon bayan juna tsakanin Sin da kasashen Afirka, musamman da yake batu ake yi na matasa, wadanda Bahaushe kan ce da su “Manyan Gobe”.

Alal hakika, Sin da kasashen Afirka, sun jima suna raya kawance da goyon bayan juna a lokutan yalwa da na tunkarar wahalhalu, kuma a matsayin ta na babbar kasa mai tasowa, Sin bata taba mantawa da abokan huldar ta na kasashen Afirka ba, inda take samar musu da tallafi ciki har da na kiwon lafiya, tare da taimakon samar da manyan ababen more rayuwa, kamar layukan dogo, da manyan hanyoyin mota, da gadoji, da cibiyoyin samar da lantarki, da filayen jiragen sama da sauran su.

La’akari da hakan ne ma, masana da dama ke ganin ko shakka ba bu, idan aka yi amfani da dandalin matasan Sin da Afirka, wajen yaukaka dangantakar sassan biyu, hakan zai kara ingiza cimma manyan nasarori a fannoni daban daban tsakanin sassan biyu, musamman ganin cewa, tuni an samar da manyan manufofin bunkasa hadin gwiwar sassan biyu, karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, da shawarar nan ta “Ziri Daya Da hanya Daya”.

Don haka dai, akwai bukatar matasan Sin da na kasashen Afirka su kara wucewa gaba wajen fadada kawance, da musaya, da hadin gwiwa tsakanin su, domin cimma kafuwar al’umma guda ta Sin da Afirka, mai makomar bai daya a dukkanin fannoni.(Saminu)