logo

HAUSA

Za a gudanar da taron tunawa da Jiang Zemin a ranar Talata

2022-12-01 21:09:06 CMG Hausa

Kwamitin tsare tsaren jana’izar Jiang Zemin, ya fitar da sanarwa da ke cewa, za a gudanar da taron tunawa da marigayin a ranar Talata 6 ga watan nan, a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing.

Da yammacin Alhamis din nan ne kuma, jirgin sama na musamman ya dauko gawar Jiang Zemin daga birnin Shanghai zuwa Beijing. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu manyan jagororin JKS, da kusoshin gwamnati, suka isa filin jirgin sama domin tarbar gawar marigayin. (Saminu Alhassan)