logo

HAUSA

Shugaban rikon kwarya na Chadi na son zurfafa hadin gwiwa tare da Sin

2022-12-01 13:12:29 CMG Hausa

Shugaban rikon kwarya na kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, ya bayyana a fadar shugaban kasar jiya Laraba cewa, ana fatan zurfafa hadin gwiwa tare da Sin daga dukkan fannoni, a kokarin kara ciyar da dangantakar dake tsakanin Chadi da Sin zuwa gaba.

Mahamat ya jajanta ci gaban alakar dake tsakanin kasashen biyu ne, a yayin da yake karbar takardar aikin da sabon jakadan kasar Sin da aka tura kasar Chadi Wang Xining ya gabatar masa. Ya kuma godewa kasar Sin bisa taimakon da ta dade tana baiwa kasarsa, inda ya jadadda cewa, bangaren Chadi na mutunta zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, kana ba zai canja aniyarsa ta bunkasa dangantakar dake tsakaninsu ba.

A nasa bangaren kuma, Wang Xining ya ce, a cikin wadannan shekarun da suka gabata, dangantaka a tsakanin Sin da Chadi ta bunkasa cikin sauri, ana ta samun amincewar juna a fannin siyasa, baya ga samun kyawawan sakamako daga dukkan fannonin bisa hadin kansu na a zo a gani. Sin na fatan karfafa mu’ammala da kokari tare da Chadi, wajen sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, ta yadda za a samar da karin sakamako da za su amfani jama’arsu.(Safiyah Ma)