logo

HAUSA

AU ta aike da tawagar musamman domin sanya ido kan shirye-shiryen babban zaben Najeriya dake tafe

2022-12-01 13:47:58 CMG Hausa

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta aike da wata tawagar siyasa ta musamman zuwa Najeriya, domin sanya ido kan shirye-shiryen dake gudana game da babban zaben kasar dake tafe.

Sashen kungiyar AU mai kula da harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata cewa, tawagar zaben, karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu kana mamba a kungiyar masanan AU, Phumzile Mlambo-Ngcuka, za ta kasance a Abuja, babban birnin Najeriya ne daga ranar 26 ga watan Nuwamba zuwa 4 ga watan Disamba.

Kungiyar ta ce, tawagar da aka tura gabanin babban zaben Najeriya dake tafe, ta kunshi shugabannin majalisar dokokin Afrika, da ma'aikatan hukumar AU da kuma kwararru masu zaman kansu a harkar zabe.
A ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 ne, Najeriya za ta gudanar da babban zabe, inda za a zabi shugaban kasa, sai kuma zaben 'yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar 11 ga Maris din shekarar 2023.(Ibrahim)