logo

HAUSA

Akwai alakar tattalin arziki mai karfi tsakanin Sin da Turai

2022-12-01 20:00:31 CMG Hausa

A wajen taron manema labarai da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta shirya a yau Alhamis, yayin da take amsa tambayar da ta shafi hadin-gwiwar Sin da Turai a fannin tattalin arziki da kasuwanci, mai magana da yawun ma’aikatar Shu Jueting ta bayyana cewa, kasarta na maida hankali sosai wajen bunkasa alakarta da kasashen Turai, da dukufa kan zurfafa hadin-gwiwarsu ta cimma moriyar juna, a wani kokari na tabbatar da samar da isassun kayayyaki a duniya, da kiyaye zaman doka da oda ta fuskar tattalin arziki da kasuwancin kasa da kasa.

Rahotannin sun ce, a karkashin jagorancin shugabannin bangarorin biyu, akwai alakar tattalin arziki mai karfi tsakanin Sin da Turai a halin yanzu. Daga watan Janairu zuwa Oktobar bana, jimillar kudin cinikayyar su ta kai dala biliyan 711.4, adadin da ya karu da kaso 6.3 bisa dari. Kasar Sin ita ce babbar abokiyar cinikayya ta farko ga kungiyar tarayyar Turai wato EU, yayin da EU din ke ci gaba da zama babbar aminiyar cinikayya ta biyu ga kasar ta Sin. (Murtala Zhang)