logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bukaci a tsaurara matakan tsaro a kusa da iyakokin tafkin Chadi

2022-11-30 10:59:43 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci da a kara sanya ido da tsarurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar, inda ya janyo hankali game da karuwar makamai, da albarusai da sauran makamai da ke karakaina a yankin tafkin Chadi.

A lokacin da yake jawabi a yayin taron shugabannin yankin tafkin Chadi (LCBC) karo na 16 da aka gudanar a Abuja, fadar mulkin kasar, shugaba Buhari wanda kuma shi ne shugaban taron kolin shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen yankin, ya bayyana cewa, an yi nasarar shawo kan barazanar da ‘yan ta’adda ke yi a yankin, yayin da kwararar makamai ke haifar da sabon kalubale.

Ya ce, duk da nasarorin da dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) suka samu da kuma ayyukan da sojojin kasar ke gudanarwa a yankin, har yanzu yankin na fuskantar barazanar ta’addanci. Ya kara da cewa, kaso mai yawa na makamai da albarusan da aka sayo don aiwatar da yaki a Libya, na ci gaba da kwarara zuwa yankin tafkin Chadi da sauran sassan yankin Sahel.

A cewarsa, rundunar MNJTF, wadda ta kunshi sojojin hadakar mambobin kasashen LCBC, ta cancaci yabo, duba da yadda ayyuka daban-daban da suke gudanarwa, suka kawo zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.(Ibrahim)