Ya dace duniya ta hada kai don magance sauyin yanayi
2022-11-30 08:50:14 CMG Hausa
Wani batu dake kara janyo hankalin duniya shi ne, matsalar sauyin yanayi. Wannan ne ma ya sa taron COP27, na sassa da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, da aka kammala a Masar ba da dadewa ba, ya cimma matsayar kafa wani asusun musamman da nufin agazawa kasashen da wannan matsala da fi shafa. Taron na Sharm El-Sheikh na kasar Masar, ya zamo wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci. Sai dai kuma a cewar babban sakataren MDD Antonio Guterres, duk da cewa, kudaden da ake fatan tarawa ba za su isa ba, yunkurin tara kudaden kadai, tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce.
Haka kuma taron ya kasance wata babbar dama ga daukacin masu ruwa da tsaki, na hada karfi da karfe wajen lalubo dabarun gaggauta na shawo kan kalubalen sauyin yanayi, ciki kuwa har da dabarun rage radadin sauyin yanayin, da gano fasahohin jurewa da dorewar rayuwa tare da kalubalen, da rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa, da ma batun samar da kudaden gudanar da wadannan ayyuka.
Nahiyar Afirka dai na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi karancin sinadarai, da iska mai gurbata muhalli a duniya, amma a hannu guda, nahiyar na sahun gaba wajen dandana kuda daga mummunan tasirin sauyin yanayi.
Masharhanta na ganin duba da yadda kasar Sin ke kan gaba, wajen cin gajiya daga fasahohin dakile sauyin yanayi, musamman fannin bunkasa amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbata muhalli, da wadanda ake iya sabuntawa. Kuma kasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga kasashen Afirka a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci ya yi da kasashen na Afirka za su fadada koyi daga kasar Sin a wannan fanni.
Ko shakka babu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin kasashen nahiyar Afirka na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a daya bangaren kasar Sin ke da kwarewa, da fasahohin bunkasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi hadin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.
Baya ga fannin raba fasahohi da kasashen Afirka, fannin samar da kudaden dakile tasirin sauyin yanayi, shi ma muhimmin bangare ne da kasashen Afirka za su iya cin gajiya daga Sin, kasancewar dama akwai kyakkyawar dangantaka, da cudanya tsakanin kasashen Afirka da Sin karkashin dandalin FOCAC na bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma irin tallafi na samar da manyan ababen more rayuwa da kasashen Afirka ke samu daga Sin, karkashin manufofin samar da ci gaba na shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Wadannan hujjoji na kara nuna muhimmancin aza kyakkyawan mafari, na ingiza hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kare muhalli, da bunkasa cin gajiya daga nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa. Kana idan har mafarkin kafa wannan asusu ya tabbata tare da aiwatar da shi kamar yadda aka tsara, da ma sauran matakai da tsare-tsare da cika alkawura to, wata rana batun matsalar sauyin yanayi za ta kasance tarihi. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)