logo

HAUSA

Najeriya tana tsakiyar yin alluran riga kafin COVID-19

2022-11-30 11:04:16 CMG Hausa

Shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko ta Najeriya (NPHCDA) Faisal Shu’aib, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu Najeriya tana tsakiyar yiwa al’ummarta alluran riga kafin cutar COVID-19.

Shugaban hukumar wanda ke kula da alluran riga kafi a kasar, ya shaidawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar cewa, ya zuwa yanzu an yiwa rabin ‘yan kasar cikakken riga kafin. Sai dai duk da wannan nasarar da aka samu, har yanzu yawan wadanda aka yiwa riga kafin bai kai burin da gwamnati ke fatan cimmawa, na yiwa kaso 70 cikin 100 na al’ummarta cikakken riga kafin nan da watan Disamban shekarar 2022 ba.

Shu’aib ya kara da cewa, kashi 13.2 cikin 100 na mutanen da aka yiwa riga kafi a kasar, sun karbi allura ta uku dake kara kariya daga cutar. Yana mai cewa, an samu raguwar masu kamuwa da cutar a kasar, da kuma ci gaba da raguwar masu shigo da cutar daga wasu kasashen waje a cikin watanni 6 da suka gabata. Haka kuma ba a samu sabbin masu kamuwa da cutar ba tun ranar 20 ga watan Nuwanba zuwa yanzu.(Ibrahim)